Drogba ya mai da martani ga masu ihu

Didier Drogba
Image caption Didier Drogba ya mayar da martani ga masu ihun wariyar launin fata

Dan wasan gaban Galatasaray, Didier Drogba, ya mayar da martani ga wadanda su ka yi masa ihun nuna wariyar launin fata yayin wasan da ya yi zafi ranar Lahadi tsakanin kungiyar da Fenerbahce.

Yayin wasan, an yi wa Drogba da abokin wasansa Emmanuel Eboue ihun biri.

A martanin da ya rubuta a shafin Facebook na kungiyar tasa, Drogba ya ce: "Kun kira ni biri, amma kun manta da dan uwa na da ya ci muku kwallaye har biyu".

Dan wasan yana magana ne a kan dan Kamaru Pierre Webo, wanda ya zura kwallaye biyun da Fenerbahce ta ci a wasan da ta lashe da biyu da daya.

An bayar da rahoton cewa wani daga cikin magoya bayan kungiyar ya mika wa Drogba da Eboue ayaba yayin wasan da aka buga a filin wasa na Sukru Saracoglu da ke Santanbul.

Drogba dai ya tafi Galatasaray ne daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China a watan Janairu, kuma ya ci kwallaye biyar a sabuwar kungiyar tasa a kakar wasanni ta bana.

Karin bayani