Ferdinand ya yi ritaya daga Ingila

Rio Ferdinand
Image caption Mai tsaron bayan Ingila Rio Ferdinand ya ce ya yi ritaya daga gasar kasa-da-kasa

Mai tsaron baya na tawagar kwallon kafa ta Ingila, Rio Ferdinand, ya bayar da sanarwar yin ritaya daga kwallon kafar kasa-da-kasa.

Dan wasan na Manchester United mai shekaru 34 a duniya, wanda ya samu bugawa kasarsa har sau 81, ya ce yana so ne ya mayar da hankali a kan sana'arsa ta bugawa kungiyarsa wasa.

A cewarsa, "bayan tunani mai zurfi, na yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zan yi ritaya daga wasan kwallon kafar kasa-da-kasa".

Kocin Ingila, Roy Hodgson, ya ce kasancewar Ferdinand ya yi kyaftin wa tawagar kasarsa, kuma ya buga Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya har sau uku, ya shiga wani ayarin 'yan wasa na musamman.

Tun bayan wasan da Ingila ta buga da Switzerland a 2011 na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta 2012, Ferdinand bai sake bugawa Ingila ba.

Hodgson ya sake kiransa ya buga wasan neman gurbi a Gasar Cin Kofin Duniya da Ingila ta buga da San Marino a watan Maris, amma daga bisani ya janye saboda wadansu dalilai.

Ferdinand ne dai ya taimaka wa Manchester United ta sake lashe Gasar Premier.

Karin bayani