Aubameyang ne gwarzon dan wasan Africa

 Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon
Image caption Aubameyang ya taimaka wa Saint-Etienne ta dauki kofi

An zabi dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na Afrika a gasar lig din Faransa ta 2012/13.

Dan wasan da ake yi wa lakabi da David Beckam na Gabon ya ci kwallaye 19 a wasanni 35.

Kuma ya taimaka wa kungiyarsa ta Saint Etienne ta dauki kofin Kalubale na Faransa.

Paris Saint-Germain ce ta dauki kofin gasar lig din kasar ta Faransa.