Fasahar bakin raga a Gasar Premier

Fasahar bakin raga ta Hawk-Eye
Image caption Fasahar bakin raga ta Hawk-Eye tana bibbiyar kwallo don gano ko ta ketare layi

Gasar Premier ta Ingila ta kada kuri'ar amincewa a fara amfani da fasahar bakin raga daga kakar wasanni ta 2013 zuwa 2014.

Tuni ma dai aka baiwa kamfanin Hawk-Eye na Burtaniya kwangilar samar da fasahar.

Fasahar Hawk-Eye dai tana amfani da kyamarori bakwai ne a kowacce raga wadanda ke sa ido a kan kwallo, kuma kamfanin ya yi ikirarin cewa tsarin "ya tabbatar da cewa sake kallon hotunan bidiyon da aka nada ba zai iya karyata awonta ba".

Manyan kungiyoyin kwallon kafa ne dai su ka kada kuri'ar amincewa a yi amfani da fasahar yayin wani taro na shugabannin Gasar Premier ashirin ranar Alhamis.

Karin bayani