Jupp Heynckes zai yi ritaya

Jupp Heynckes
Image caption Heynckes ya ce, ''idan da ban kai haka ba da shekaru 15 da sai na yi tunanin zuwa wata kasa aiki''

Mai horad da 'yan wasan Bayern Munich Jupp Heynckes ya nuna aniyarsa ta yin ritaya daga aiki baki daya.

Ya ce ba zai sake aikin horad da wata kungiya a Bundesliga ba kuma yanzu ya yi tsufa ya je wata kasar waje aiki.

A watan Yuni ne Pep Guardiola zai maye gurbin Heynckes mai shekaru 68 bayan da ya kai Bayern ga daukar kofin lig din Jamus Bundesliga.

Da kuma kai kungiyar zuwa wasan karshe na Kofunan Zakarun Turai da na kalubalen kasar.

Kociyan ya ce ranar Asabar ce za ta zama ranar wasansa na karshe a Bundesliga a matsayin mai horad da 'yan wasa.

A ranar Asabar din ne Bayern za ta yi wasanta na lig na karshe na bana a gidan tsohuwar kungiyar Heynckes Monchengladbach.

Sannan ranar 25 ga watan Mayu za ta yi wasan karshe na Zakarun Turai a Wembley da Borussia Dortmund.

Kana kuma ta yi wasan karshe na Kofin Kalubale na Jamus da Stuttgart a Berlin ranar 1 ga watan Yuni.

Arjen Robben

A wani labarin kuma dan wasan Bayern Munich din Arjen Robben ya ce ba shi da niyyar bin sahun Heynckes na barin kungiyar.

Dan wasan mai shekaru 29 ya bayyana hakan ne sakamakon rade radin da ake yi cewa zai koma Manchester City.

Ya ce ''ban damu da wannan jita-jita ba, ko da yaushe akan yada jita-jita da dama.

Har yanzu ina da sauran shekaru biyu a kwantiragina, saboda me zan tafi ?''