Chelsea ta dauki kofin Europa

Chelsea ta dauki Kofin Europa
Image caption Benitez zai bar Chelsea bayan wasansu ranar Lahadi cike da alfaharin daukar Kofin na Europa

Chelsea ta dauki kofin Europa bayan da ta yi nasara a kan Benfica da ci 2 a Amsterdam.

Hakan ta sa Rafeal Benitez zai kammala aikinsa na kociyan rikon kwarya na kungiyar da gagarumar nasara ta kafa tarihin daukar kofin.

Fernando Torres ne ya fara daga ragar Benfica a minti na 59 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Oscar Cardozo ne ya ramawa Benfica da bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan minti 11.

Peter Cech ya yi kokarin kare wata kwallon da Cardozo ya kai hari don farke kwallon amma hakarsa bata cimma ruwa ba.

Daga nan kuma sai Frank Lampard ya kai wani wawan hari da kwallon ta bugi sandar raga ta dawo.

A 'yan dakikokin wasan na karshe bayan karin mintuna uku na bata lokaci ne Branislav Ivanovic ya ci kwallo ta biyun da kai a wani bugun gefe da Juan Mata ya dauko.

Ivanovic wanda shi ne kyaftin din Serbia ya ci kwallaye 18 ke nan a bana biyar daga cikinsu a Premier, kuma shi ne gwarzon dan wasan kasar na shekara

Sau bakwai ke nan a jere Benfica tana kasa daukar wani kofin Turai.