David Beckam zai yi murabus bana

David Beckam
Image caption Beckam ya ce ''na godewa PSG da ta bani dama na ci gaba amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi murabus''

Tsohon Kaftin din kungiyar wasan kwallon kafar Ingila David Beckham zai yi murabus a karshen kakar wasa ta bana.

Beckham mai shekaru 38 ya bugawa Ingila wasa sau 115 Manchester United kuwa ya yi mata wasanni 394, inda ya dauki Kofin Premier 6 da kuma na Zakarun Turai da kungiyar.

Bayan Manchester United da PSG ya yi Real Madrid da LA Galaxy ta Amurka da kuma AC Milan inda gaba daya ya dauki kofuna 19 da suka hada da guda 10 na lig-lig.

Dan wasan na tsakiya ya fara bugawa Ingila wasa a 1996 da Moldova kuma ya rike mukamin kyaftin din kasar daga 2000 zuwa 2006.

Wasan karshe da ya yi wa Ingila shi ne wanda kasar ta ci Belarus 3-0 a 2009.

A watan Janairu dan wasan ya kulla yarjejeniyar yi wa Paris St-Germain wasa na watanni 5 kuma ya sadaukar da albashinsa na sabbin Zakarun lig din Faransan ga aikin bada taimako.