Benitez yana alfahari da Chelsea

Image caption Rafael Benitez

Kocin Chelsea, Rafael Benitez, ya ce yana alfahari da kasancewarsa a kulob din bayan da ya jagoranci kungiyar ta lashe Gasar Nahiyar Turai watau Europa League.

Tsohon kocin na Liverpool na fuskantar tsana daga wadansu magoya bayan Chelsea tun bayan da ya maye gurbin Roberto Di Matteo a watan Nuwamba.

Sai dai Benitez ya jagoranci kungiyar har ta cancanci shiga Gasar Zakarun Turai, kuma ya taimakawa kulob din ya yi nasara a wasan da suka buga da Benfica inda suka tashi 2 da 1, a wasan karshe na lashe Gasar Nahiyar Turai da aka yi a filin wasa na Amsterdam Arena.

Benitez ya ce: " Wannan al'amari ne da mutum zai yi alfahari da shi a matsayinsa na koci."

Benitez ya cancanci yabo

Mai tsaron baya na Chelsea, Gary Cahill, ya ce Rafael Benitez ya cancanci yabo bayan da ya taimakawa kulob din ya lashe Gasar Nahiyar Turai.

Ya ce: " Mun samu ci gaba fiye da a baya a Gasar Nahiyar Turai, domin kuwa yanzu mun dauki kofi. Don haka ya kamata a jinjinawa Benitez saboda wannan matsayi da muka samu".