A wata uku za a share fagen Gasar Afirka

Shugaban CAF Isa Hayatou
Image caption Shugaban hukumar CAF Isa Hayatou

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta ce a cikin watanni uku kacal na badi za a yi wasannin neman gurbi a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2015.

Hakan dai na nufin za a cunkusa wasanni 144 tsakanin tawagogin kasashe 48 a rukunoni 12 tsakanin watan Satumba zuwa na Nuwamba.

An tsara wannan jadawali ne kuwa don ya dace da kalandar Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA.

Babu wasanni a 2014 kafin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya wadda za ta gudana a Brazil.

Wannan ne karo na farko da ake tsara wasannin share fagen don su dace da Gasar Cin Kofin Duniya tun bayan da aka sauya kalandar gasar ta Afirka zuwa shekaru mara.

Sai dai matsalar sufuri da ake fuskanta a wadansu kasashen nahiyar Afirka—musamman tsakanin gabashi da yammacin nahiyar—ka iya yin tarnaki ga matsattsen jadawalin.

Karin bayani