Ancelotti ya bukaci tafiya daga PSG

Carlo Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti ya jagoranci PSG suka dauki Kofin lig din Faransa a bana na farko tun 1994

Kociyan Paris St-Germain Carlo Ancelotti da Real Madrid ke harin dauka ya bukaci barin kungiyar amma kuma shugabanta ya ce ba za ta sabu ba.

A kwanakin da suka gabata Ancelotti mai shekaru 53 ya gabatarwa da PSG bukatarsa ta tafiya Real Madrid.

Kamar yadda shugaban zakarun Lig din Faransan Nasser al-Khelaifi ya ce ''amma muka ce masa yana da sauran shekara daya,saboda haka sai yadda muka yi shawara.''

Shugaban ya kara da cewa ''matsalarsa ce ba tamu ba mun kara masa shekara daya a kan wadda ta rage masa ma.

Ya kara da cewa, Idan kana da kwantiragi a kanka kamata ya yi ka mutunta yarjejeniyar.''