Keegan bai ji dadin korar Mancini ba

Kevin Keegan
Image caption A watan Afrilu Keegan ya shawarci Man City kada su sallami Mancini ko ba su dauki kofi ba.

Tsohon mai horad da 'yan wasan Manchester City Kevin Keegan ya soki lamirin kungiyar na sallamar kocinta Roberto Mancini.

A ranar Litinin da ta wuce klub din ya kori Mancini mai shekaru 48 dan kasar Italiya wanda ya jagoranci kungiyar ta dauki Kofin Premier bayan da Wigan ta yi galaba a kansu a wasan karshe na Kofin FA.

Keegan mai shekaru 62 ya ce: ''ai ba za su iya cewa bai yi kokari ba. Kofuna uku a shekaru uku ga kungiyar da ba ta ci komai ba abin takaici ne.''

Tsohon kociyan na Ingila ya horad da 'yan wasan Manchester City daga 2001 zuwa 2005.

Ya ce ba dai-dai ba ne kungiyar ta ce ta kori Mancini a kan zargin mummunar dangantaka tsakaninsa da 'yan wasa a matsayin dalilin sallamarsa.

Shi ma kociyan Manchester United da ya yi murabus Sir Alex Ferguson ya soki Man City din a kan korar Mancini.