Kamaru na daf da nada sabon koci

Kocin Kamaru mai barin gado Jean-Paul Akono
Image caption Hukumar Fecafoot ta ce tana daf da nada kocin da zai maye gurbin Jean-Paul Akono

Kamaru na daf da nada sabon kocin da zai maye gurbin Jean-Paul Akono.

An tsegunta wa BBC cewa Raymond Domenech da Antoine Kambouare ake duba yiwuwar baiwa mukamin.

A makon jiya ne dai Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru (FECAFOOT) ta ce Akono zai ci gaba da rike mukamin nasa har zuwa lokacin da za a buga wasannin neman gurbi a Gasar Cin Kofin Duniya a watan Yuni yayin da za a ci gaba da farautar wanda zai gaje shi.

Sai dai tuni wani kakakin Ma'aikatar Wasanni ta Kamaru ya shaida wa BBC cewa "lamura za su sauya daga ranar 20 ga watan Mayu".

Domenech, dan Faransa mai shekaru sittin da daya da haihuwa, shi ne kocin tawagar kasarsa daga shekarar 2004 zuwa 2010, kuma ya kai 'yan wasan kasar matsayi na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya na 2006.

Sai dai bai taba aiki a bangaren kwallon kafar Afirka ba a ko wanne mataki, kuma tun bayan karshen aikinsa da tawagar kwallon kafa ta Faransa bai jagoranci wata harkar kwallo ba.

Shi ma Kambouare ba shi da wata harka yanzu, kasancewar kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal ta Saudi Arabia ta sallame shi a watan Janairun bana.

Shi ma dai Kambouaren, wanda tsohon kocin Paris Saint Germain ne, ba shi da kwarewa a harkar kwallon kafar Afirka. Shekarunsa 49 da haihuwa.

Bajamushe Volker Finke da dan Faransa Pierre Lechantre ma an gana da su, amma an yi amanna cewa za a yi ba su.

A halin da ake ciki kuma, hukumar FECAFOOT ta tuntubi 'yan wasan da ke cikin tawagar da Akono ya zaba don su buga wasan sada-zumunta da Ukraine ranar 2 ga watan Yuni da kuma wasan neman gurbi a Gasar Kofin Duniya wadanda Kamaru za ta buga da Togo ranar 9 ga watan Yuni da wanda za ta buga da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ranar 16 ga watan Yuni.

Bayan Akono ya sanar da wadanda ya zaba FECAFOOT ta bayyana cewa ta yi watsi da zabin nasa saboda tana sa ran daukar sabon koci wanda zai yi nasa zabin.

Amma yanzu an shaida wa BBC cewa sabon kocin zai yi aiki ne da wadanda Akono ya zabo.

Karin bayani