Mourinho zai tafi a wata mai zuwa

  • 20 Mayu 2013
Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho da Real Madrid an rabu

Real Madrid ta sanar cewa kociyanta Jose Mourinho zai bar Kungiyar a karshen kakar wasannin da ke karewa bayan shekaru uku a cikinta.

Shugaban klub din Florentino Perez shi ne ya sanar da labarin a madadin kungiyar tare da yabawa a kan abin da ya kira aiki tukura da kociyan ya yi a kungiyar.

Perez ya ce, ''mun yanke shawarar kawo karshen dangantakarmu, babu wanda aka kora, yarjejeniya ce da kowa ne bangare ya amince da ita.''

Yanzu dai maki 13 ne tsakanin Barcelona ta daya a lig da Real Madrid ta biyu, kuma ranar Juma'a Atletico Madrid ta cinye us a wasan karshe na Kofin Kalubale na kasar.

Haka kuma Real Madrid din sun sha kashi a wasannin kusa da karshe na Gasar Zakarun Turai a cikin shekaru uku da Mourinho ke jagorantarsu.

Wasanni biyu suka rage wa kungiyar na lig na bana, ranar 26 ga watan Mayu za ta je gidan Real Sociedad.

Sannan a ranar 1 ga watan Yuni a gida Bernabeu Mourinho zai yi aikinsa na karshe da klub din a haduwarsu da Osasuna.

Tsohon kociyan Chelsea Carlo Ancelotti na Paris St-Germain yanzu shi ake rade radin zai gaje shi a Real Madrid.

Aamma kuma shugaban Real din Perez ya musanta hakan da cewa ba su zabi magajinsa ba kawo yanzu, yace ''abu ne da zamu duba a kwanakin da ke tafe.''

Ita kuma kungiyar Chelsea da ake cewa Mourinho zai koma mata kociyanta Rafeal Benitez mai barin gado ana rade radin zai koma Paris St-Germain.

Dangantaka ta yi tsami

A shekara ta 2016 ne da kwantiraginsa da klub din za ta kare bayan da aka sabunta ta sakamakon nasarar da ya samu a gasar La Liga a bara.

Amma kuma rashin daukar wani kofi a bana ana ganin shi ya sa dangantakarsa da klub din ta yi tsami.

Shi kansa ya bayyana kakar wasannin ta bana a matsayin mafi muni a rayuwarsa.

Baya ga wannan Mourinho mai shekara 50 dangantakarsa da fitattun 'yan wasan kungiyar irin su Iker Casillas da Sergio Ramos da Pepe ta yi tsami.