Moyes na ganawa da ma'aikatan Man United

David Moyes da Sir Alex Ferguson
Image caption Moyes ya ce, ''watakila zan rika yin ayyuka biyu ne a makon nan ko ma zuwa gaba''

Sabon kociyan Manchesteer United David Moyes yana ganawa da wasu ma'aikatan bangaren horad da 'yan wasan kungiyar a ranar Litinin din nan.

Ana ganin kociyan dan Scotland zai gana da mai horad da masu tsaron gida Eric Steele da kuma Rene Meulensteen da ke horad da manyan 'yan wasan kungiyar.

Sabon kociyan zai kuma gana da wasu mai'aikatan sashen bada horon amma dai ba a tsammanin zai yi wasu manyan sauye-sauye.

A ranar Lahadi Moyes ya jagoranci wasan Everton na karshe amma kuma sai a ranar 1 ga watan Yuli zai maye gurbin Sir Alex Ferguson a hukumance.

A watan Yuli Manchester United za ta yi rangadin wasanni a Thailand da Australia da Japan da kuma Hong Kong.

Wasan klub din na kofi na farko karkashin Moyes zai kasance ne a Wembley ranar 11 ga watan Agusta na Community Shield da Wigan wadda ta dauki Kofin FA.