Dole mu rike Bale: Kociyan Tottenham

Gareth Bale
Image caption Gareth Bale ne ya ci wa Tottenham kwallonta da Sunderland a wasan karshe na Premier

Mai horad da 'yan wasan Tottenham Gareth Bale Andre Villas-Boas ya ce dole ne kungiyar ta rike Gareth Bale idan tana son ci gaba a kakar wasa ta gaba.

Ana ganin Real Madrid da sauran kungiyoyin da suka samu damar shiga Gasar Zakarun Turai ta gaba suna harin sayen Bale a lokacin sayen 'yan wasa.

Tottenham ta kasa samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai ta gaba bayan da Arsenal ta kammala Gasar Premier a matsayi na hudu ita kuma tana matsayi na biyar.

Rashin samun wannan dama ya sa ana shakkun ci gaba da zaman dan wasan mai shekaru 23 a klub din.

Sai dai Villas-Boas ya ce ''idan dai har muna son taka rawar da tafi ta bana dole ne mu rike gwanayen 'yan wasanmu wannan shi ne abin da shugabannin klub din suka sheda min.''

Maki 72 da kungiyar ta kammala Premier da su sun zarta na kakar wasa ta 2009-10 inda ta gama da maki 70.

Amma kuma ta samu cancantar shiga Gasar Zakarun Turai bayan da ta kammala a matsayi na hudu a Premier.