Messi ya nemi Barca kar ta sauya wasa

Lionel Messi
Image caption Lionel Messi ya ce, ''ba koda yaushe ake nasara ba''

Lionel Messi ya bukaci Barcelona da ta ci gaba da tsarin wasanta duk da cewa ta kasa daukar Kofin Zakarun Turai na bana.

Kungiyar Bayern Munich ta Jamus ta lallasa Barcelona a wasan kusa da na karshe na gasar 7-0 gida da waje.

Sakamakon ya sa wasu ke ganin tsarin wasan 'yan Jamus ya zarta na 'yan Barcelonan, na tattaba kwallo a tsakanin 'yan wasa ko bani-im-baka.

Game da hakan Messi mai shekaru 25 ya ce, '' ba zamu dimauce ba, ba zamu sauya tsarin wasanmu ba, saboda ai ba koda yaushe ne ake samun nasara ba.''

Gwarzon dan wasan na duniya, ya ce, ''shekara da shekaru muna irin wasanmu kuma kociyoyi da kungiyoyi sun nazarce shi, kamata ya yi mu natsu mu maida hankalinmu a kan shekara ta gaba.''

Sai dai shi kuma dan wasan baya na Barcelonan Gerard Pique yana ganin lalle akwai bukatar klub din ya sauya tsarin wasan nasa.

Ya ce, '' yanzu ba mu ne kan gaba ba, wasu sun zarta mu.''

Mataimakin shugaban kungiyar Josep Bartomeu yana ganin klub din na bukatar sayo sababbin 'yan wasa hudu ko biyar.