Za a rufe filin wasan Roma

Roma Fans
Image caption Roma ta ce tana kokarin gano magoya bayan da suka aikata laifin

Za a rufe wani sashe na filin wasan Roma a lokacin wasa daya a kakar wasanni ta gaba bayan da magoya bayan kungiyar suka sake rera wakokin nuna wariyar launin fata a kan Mario Balotelli.

Magoya bayan sun sake aikata hakan ne a lokacin wasansu da Napoli ranar Lahadi a lokacin da labari ya zo musu cewa Balotelli ya ci bugun fanareti.

Wanda kungiyarsa ta yi galaba 2-1 a Siena abin da ya taimakawa klub din samun damar shiga Gasar Zakarun Turai.

Klub din ya maida martani da alkawarin haramtawa duk wanda aka gano da laifi mu'amulla da shi.

Sashen da za a rufe na magoya bayan kungiyar ne 'yan gani-kashe-ni.

A baya an ci tarar Roma fam 42,400 bayan dakatar da wasansu da kungiyar AC Milan ta Balotelli, aka sake ranar 12 ga watan Mayu saboda rera wakokin wariyar launin fata a lokacin.

A makon da ya wuce Balotelli wanda ya ci kwallaye 12 a wasanni 13 tun lokacin da ya koma AC Milan daga Manchester City a watan Janairu ya yi barazanar fita daga fili duk lokacin da aka sake cin mutuncinsa ta wariyar launin fata.