Tsohon dan wasan Man United ya mutu

Brian Greenhoff
Image caption Burin Brian Greenhoff ne ya yi wa Manchester United wasa

Tsohon dan wasan Manchester United da Ingila Brian Greenhoff ya mutu kwatsam yana da shekaru 60.

Dan wasan na daga cikin tawagar Manchester United da ta doke Liverpool a wasan karshe na gasar Kofin Hukumar Kwallon Ingila FA ta dauki kofin a 1977.

Kafin ya koma Leeds a kan fam 350,000 a 1979 wanda ba karamin kudi ba ne a lokacin, ya yi wa United wasanni 271.

Sannan ya ci kwallaye 17 kuma ya yi wa Ingila wasanni goma sha takwas.

Wasansa na farko da ya buga wa Ingila shi ne da Wales ranar 8 ga watan Mayu a 1976 kuma na karshe da Australia ranar 31 ga watan Mayu na 1980.