Murray ya janye daga French Open

Andy Murray
Image caption Ciwon baya ya tilasta wa Andy Murray janyewa daga gasar French Open

Andy Murray ya janye daga gasar French Open sakamakon ciwon bayan da ya tilasta masa janyewa a Italiya makon jiya.

Dan wasan tennis din na biyu a duniya ya janye a wasan shi na farko a Rome, sannan kuma ya yanke shawarar ba zai shiga fili a Paris ba.

Murray na fatan zai murmure kafin fara gasar Aegon a filin Queen's Club dake London ranar 10 ga watan Yuni.

"Yanke wannan sahawara abu ne mai matukar wahala", inji Murray, wanda ya kara da cewa, "Ga shi ina matukar kaunar yin wasa a Paris, amma bayan shawara da likita ba zan iya bugawa ba.

"Ina neman afuwar masu shirya gasar, ina kuma godiya ga dukkanin mutanen da suka aiko min sakon fatan alheri. Yanzu abin da zan mai da hanakli a kai shi ne sake shiga fili da zarar hali ya yi".

Wannan ce babbar gasa ta farko da Murray zai kaurace mata tun bayan gasar Wimbledon ta 2007.

Ranar Lahadi za a fara gasar ta French Open, wacce ita ce babbar gasa ta biyu a bana.

Karin bayani