Manuel Pellegrini zai bar Malaga

Manuel Pellegrini da Roberto Mancini
Image caption Ana saran Pellegrini zai gaji Mancini a Man City

Kociyan da Manchester City ke harin dauka Manuel Pellegrini na Malaga ya ce zai bar kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana.

Sanarwar tasa ta bude hanyar tafiyarsa Manchester City inda ake ta saran zai koma domin maye gurbin Roberto Mancini.

Kociyan mai shekaru 59 ya ce ba wai zai bar kungiyar ba ne saboda burin samun kudi sai dai kawai domin cimma wani fata nasa.

A ranar Lahadi ne Pellegrini zai jagoranci Malaga a wasan karshe a Rosaleda.

Kociyan dan kasar Chile a baya ya horad da 'yan wasan Villareal da Real Madrid.

Ya jagoranci Malaga zuwa wasan dab da na kusa da karshe na Gasar Zakarun Turai na bana inda Borussia Dortmund ta fitar da su.