An dakatar da Mourinho da Ronaldo

Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho zai bar Real Madrid bayan shekaru uku

An haramta wa Cristiano Ronaldo da Jose Mourinho wasanni biyu bayan da alkalin wasa ya kore su a wasan karshe da Atletico.

An kori Mourinho mai shekaru 50 saboda rashin amincewar da ya nuna a kan hukuncin alkalin wasa na korar Ronaldo.

Alkalin wasan ya kori Ronaldo ne saboda kafar da ya yi wa dan wasan Atletico Gabi a fuska.

Sai dai da wuya Mourinho ya yi hukuncin saboda zai bar kungiyar ta Real Madrid.

Kuma Hukuncin bai shafi wasan lig ba sai na Kofin Kalubale na kasar.

Hukuncin hana Ronaldo wasannin biyu shi kuma daya na mugunta ne daya kuma na katin korar da aka bashi bayan daman an bashi katin gargadi a wasan.

Mourinho da Ronaldo dukkanninsu za su halarci wasannin Real Madrid din biyu na La Liga na karshe saboda hukuncin bai shafi wasan lig ba.

Wasannin kungiyar na karshe na bana sune wanda za su je gidan Real Sociedad ranar Lahadi da kuma wanda za su yi a gida a karshen mako na gaba.