Zakarun Europa za su shiga Gasar Zakarun Turai

Chelsea Zakarun Europa
Image caption Chelsea ta dauki Kofin Europa na farko a 2013

A ranar Juma'ar nan Hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA zata sanar ko duk kungiyar da ta dauki kofin Europa za a bata damar shiga gasar Zakarun Turai daga 2015.

Wannan wani shiri ne da ake yi da nufin kara armashin gasar Kofin Europa wanda Chelsea ta dauka a farkon watan nan.

Sabuwar dokar za ta sa Ingila ta iya samun kungiyoyi 5 a Gasar Zakarun Turai daga 2015-16 idan daya daga cikin kungiyoyinta ta dauki Kofin Europa a 2015 kuma ba ta cikin guda 4 na farko a Premier.

A yanzu kungiyoyin da suka gama a matsayin na uku a rukuninsu na Gasar Zakarun Turai su na fada wa Gasar Europa.

Kamar yadda Chelsea da Benfica da suka yi wasan karshe na Europa na bana suka yi.

Wigan da Swansea da Tottenham su ne za su wakilici Ingila a gasar Europa ta gaba.

Gasar ta Europa dai ba ta samar da kudi sosai da kuma samun yayatawa a kafafen yada labarai kamar ta Zakarun Turai.

A halin da ake ciki kuma an bayyana filin wasan Olympic na Berlin a matsayin inda za a yi wasan karshe na Gasar Zakarun Turai ta 2015.

Shi kuma wasan karshe na Gasar Europa na shekarar za a yi shi ne a babban filin wasa na Warsaw dake Poland.