Ferdinand ya sabunta kwantiragi

Rio Ferdinand
Image caption Ferdinand ya dauki kofuna goma da Man United

Rio Ferdinand ya kara kwantiragin shekara daya da Manchester United abin da ya kawo karshen rashin tabbas din da ake yi game da ci gaba da zamansa a kungiyar.

A makon da ya wuce ne ya bayyana murabus dinsa daga buga wa Ingila wasa domin ya maida hankalinsa a kan klub din.

Daman tun a farkon watan nan tsohon kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce Ferdinand ya ji dadin zamansa a kungiyar kuma za a sabunta kwantiraginsa.

Dan wasan na baya ya buga wa Man United wasanni 34 a bana da suka hada da 28 na Premier, fiye da duk wani dan wasan baya na kungiyar.

Tsohon dan wasan West Ham da Leeds United da ya yi wa Ingila wasanni 81, ya koma Manchester United a watan Yuli na 2002 a kan kudi kusan fam miliyan 30.

Hakan ya sa ya zama dan wasan baya mafi tsada a duniya.