'Kofin Duniya ne babban burin Najeriya'

Shaibu Amodu
Image caption Dole samun gurbi a gasar Kofin Duniya ta zama babban burin Super Eagles, inji Shaibu Amodu

Daraktan tsare-tsare na tawagogin kwallon kafar Najeriya, Shaibu Amodu, ya ce lallai ne babban burin babbar tawagar kasar, Super Eagles, ya kasansce samun gurbi a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2014, ba kokarin lashe gasar Zakarun Nahiyoyi da za yi a watan gobe ba.

A gasar da za a yi a watan Yuni, Zakarun na Afirka za su hadu da Tahiti, da Uruguay, da Spain a Brazil; haka zalika gasar na cikin shirye-shiryen da kasar ta Brazil ke yi na daukar bakuncin Gasar Kofin Duniyar.

Sai dai Amodu, wanda ya jagoranci Super Eagles lokacin da suka kare a matsayi na hudu a gasar ta Zakarun Nahiyoyi ta farko a Saudi Arabia a 1995, ya shaida wa BBC cewa, "Ina amfanin lashe gasar da ta zama shirin Gasar Kofin Duniya, sannan a fadi ba nauyi yayin babbar gasar badi?

"kofin Duniya na da matukar muhimmanci ga kasar. Don haka a wajenmu ita ce gasa mafi muhimmanci.

"Kafofin yada labarai da 'yan kallo na sa ran ganin Najeriya ta lashe gasar ta Zakarun Nahiyoyi, amma a gaskiya a wajen 'yan wasanmu da ma kasarmu ba ta kai ta cin Kofin Duniya muhimmanci ba".

A saman rukunin neman gurbi a Gasar ta Kofin Duniya dai Najeriya na kai-da-kai da Malawi, kuma tana fuskantar wasannin waje a Kenya da Namibia a watan gobe.

Amodu na so ne 'yan wasan na Super Eagles su mayar da hankali a kan wadannan wasannin.

Karin bayani