Robson za ta kara da Wozniacki a Paris

Laura Robson
Image caption Laura Robson za ta fuskanci Caroline Wozniacki a zagaye na farko na gasar French Open

'Yar wasan tennis ta daya a Burtaniya, Laura Robson, za ta kara da tsohuwar 'yar wasa ta daya a duniya, Caroline Wozniacki, a zagayen farko na gasar French Open.

Wozniacki za ta shiga gasar ne a bisa doron kashin da ta sha har sau hudu a jere a fili mai turbaya.

Ita kuwa 'yar wasa ta biyu a Burtaniya, Heather Watson, za ta kara ne da Stefanie Voegele, yayin da Elena Baltacha za ta fuskanci Marina Erakovic.

Rashin shigar Andy Murray gasar saboda rauni na nufin babu wani dan Burtaniya da zai kara a wasannin maza a karo na farko tun 1994.

Rafael Nadal, wanda ke neman nasararsa ta takwas a gasar ta French Open, ka iya karawa da dan wasa na daya a duniya Novak Djokovic a wasan kusa da na kusa da na karshe bayan an jera su a rukuni guda.

Karin bayani