Bayern Munich ta lashe kofin zakarun Turai

Bayern
Image caption A karshen kakar bana ne kocin Bayern Jupp Heynckes zai yi murabus

Kwallon da Arjen Robben ya zira ana dab da tashi ce ta baiwa Bayern Munich takwarorinsu na Jamus Borussia Dortmund da ci 2-1 a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a filin wasa na Wembley.

Kokarin da masu tsaron gida na kungiyoyin biyu suka yi ne ya sa aka shafe mintina 60 babu ci a wasan.

Har sai da Mario Mandzukic ya zira kwallon farko a ragar Dortmund sakamakon kwallon da Robben ya bugo masa ta gefe.

Amma ba da wani bata lokaci ba Borussia suka rama ta hannun Ilkay Gundogan daga bugun fanareti bayan da Dante ya yi takun kyata ga Marco Reus.

Sai dai Robben ya zira kwallon Bayern ta biyu a minti na 88 abinda ya sanya magoya bayansu cikin murnar da suka dade basu yi irinta ba.

Wannan ne dai karo na uku da Bayern ke zuwa wasan karshe a gasar cikin shekaru hudu.

Kocin Bayern Munich Jupp Heynckes zai yi murabus inda tsohon kocin Barcelona Pepe Gaurdiola zai maye gurbinsa.

Karin bayani