Crystal Palace ta dawo gasar Premier

Image caption Wilfred Zaha ne ya samu bugun daga kai sai mai tsaron gida da Palace ta ci

Crystal Palace ta dawo gasar Premier ta Ingila bayan ta doke Watford da ci daya mai ban haushi a wasan karshen na neman gurbin daya rage a gasar Premier.

Kungiyoyin biyu dai na taka leda ne a gasar kasa dana Premier wadda ake kira Championship.

Kevin Phillips ne ya zura kwallon daya tilo da ya bawa kungiyar nasara a karin lokaci a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da Marco Cassetti ya tade Wilfred Zaha.

Watford dai ta kusan ta fanshe kwallon ana sauran wasu yan dakikai kafin a tashi wasan.

Crystal Palace dai ta yi shekaru takwas rabonta da gasar ta Premier, kuma wannan nasara da ta samu yasa ta samu kyautar fam miliyan dari da ashirin wanda zai taimaka mata idan an fara kakar wasanni na Premier a badi.