Torres ya samu shiga tawagar Spain

Dan wasan Chelsea Fernando Torres ya samu shiga tawagar SPAIN da za su yi wasa a gasar zakarun nahiyoyi da za a yi a kasar Brazil a watan Yuni.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 29 ya lashe gasar Europa da Chelsea a kakar wasan bana, kuma a yan kwananan bai samu shiga cikin yanwasan da kocin Spaniya Vincente del Bosque yake hadawa ba.

'Yan wasa takwas dake taka leda a Ingila sun samu shiga cikin tawagar mai yan wasa 26 wanda kuma za a rage zuwa 23 kafin a fara gasar daga ranar 15 ga watan Yuni.

Torres dai ya taka rawar gani sosai a kakar wasan bana a Chelsea inda ya zura kwallaye 22 a wasanni 64 da ya buga bana.