Ashley Cole zai zama kyaftin din Ingila

Ashley Cole
Image caption Hodgson ya ce ba Arsenal da Chelsea kadai Ashley Cole ya bauta wa har ma da Ingila

Ingila za ta karrama dan wasan Chelsea Ashley Cole da rike mukamin kyaftin din kungiyarta a wasan sada zumunta da za su yi da Jamhuriyar Ireland saboda cika wasanni 100 da ya buga wa kasar.

A wani taron manema labarai kociyan Ingilan Roy Hodgson ya ce Cole ne zai jagoranci 'yan wasan wurin shiga fili amma kuma Frank Lampard ne zai rike mukamin kyaftin a madadin Steven Gerrad wanda baya nan.

Amma kuma daga baya sai 'yan tawagar Ingilan suka kafe cewa Ashley Cole ne zai rike mukamin na kyaftin a wasan na ranar Laraba da daddare.

Wasan na Ingila da Jamhuriyar Ireland a Wembley shi ne na 102 da Cole zai yi wa kasar bayan zama dan wasa na 7 da ya cimma bajintar yi wa Ingila wasa sau 100 a lokacin da suka yi da Brazila watan Fabrairu.

Kuma wasan shi ne na farko tun bayan da kasashen suka hadu a filin wasan Lansdowne Road a birnin Dublin na Jamhuriyar Ireland a 1995, wasan da aka tashi kafin lokaci saboda rikicin magoya baya.

A kan wasan kociyan na Ingila Roy Hodgson ya roki magoya bayan kasar da su guji rera wakokin cin zarafi ko wadanda zasu jawo rikici.

An san magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Ingila da son rera wakokin adawa da kungiyar aware ta IRA ta Ireland.