Kawancen Sunderland da BFS

Image caption Sunderland ka iya amfani da kudin da ta samu daga kawancenta da BFS ta sayi 'yan wasa

Daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na Gasar Premier ta Ingila, Sunderland, ta bayar da sanarwar kulla wata yarjejeniyar hadin-gwiwa da reshen Burtaniya na kamfanin Bidvest Group Limited na Afirka ta Kudu.

Yarjejeniyar da aka kulla da kamfanin BFS Group ta hada da daukar nauyin rigunan 'yan wasa, da tallace-tallacen bayan fili, da kuma shigar da 'yan wasa cikin al'amuran al'umma a Burtaniya.

Babbar jami'ar gudanarwa ta kungiyar, Margaret Byrne, ta ce: "Na tabbata wannan kawance zai yi armashi, domin martabar kamfanin ta fuskar tallafa wa al'umma daidai take da tamu".

Ta kara da cewa, "Wannan yarjejeniya za ta kara kimar kungiyarmu ta fuskar kasuwancin kasa-da-kasa—yayin da Sunderland ke alfahari da tarihinta a yankin da take, idan tana so ta ci gaba, to lallai ne kungiyar ta mayar da hankali wajen fadada tasirinta a matakin kasa-da-kasa".

Kungiyar ta Sunderland dai ta yi nasarar tsallake rijiya da baya: da maki uku ta kauce wa rikitowa daga Gasar Premier a kakar wasanni ta bara.

Tuni dai kocin kungiyar, Paolo di Canio, wanda ya kama aiki a watan Maris ya bayyana aniyarsa ta yi wa tawagar 'yan wasan da ya gada daga Martin O'Neill garambawul.

Kocin dan asalin kasar Italiya yana so ne ya kawo 'yan wasa shida ko bakwai a lokacin bazara, don haka zai yi farin cikin samun kudaden da za a iya samu daga kawancen kungiyar da kamfanin BFS Group.

Karin bayani