Kolo Toure zai koma Liverpool

Kolo Toure
Image caption A shekaru 7 a Arsenal Toure ya dauki Kofin FA sau biyu kuma da shi suka dauki Premier a 2003-04

Liverpool ta amince ta dauki dan wasan Manchester City Kolo Toure.

Dan wasan mai shekaru 32 dan kasar Ivory Coast zai koma Liverpool ranar 1 ga watan Yuli lokacin da kwantiraginsa da Manchester City zai kare.

Kolo Toure wanda ya buga wa Man City wasanni 102 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Arsenal a kan fam miliyan 14 a watan Yuli na 2009 yana daga cikin 'yan wasan da Cityn ta dauki Kofin Premier a kakar wasanni ta 2011-12.

Sai dai kuma a kakar wasannin da ta kare wasanni 13 kawai ya buga wa Kungiyar kuma ba a sa shi cikin tawagar kungiyar ta Gasar Zakarun Turai ba.

Liverpool ta dauki Toure ne saboda Jamie Carragher dan bayan kungiyar ya daina wasa da kuma rashin tabbacin zaman Martin Skrtel dan Slovakia.

A shekaru 7 a Arsenal ya dauki kofunan FA biyu kuma yana cikin tawagar Arsenal da ta dauki Premier a 2003-04 ba tare da an ci su ko da sau daya ba.

Sai dai Kolo Touren ba ya cikin 'yan wasan Manchester City da suka dauki Kofin FA na 2011 saboda an dakatar da shi tsawon watanni 6 saboda samunsa da laifin amfani da kwayoyin da aka haramta.