Eto'o ba zai yi wasan sada zumunta ba

Samuel Eto'o
Image caption Kyaftin Samuel Eto'o ba zai buga wasan sada zumunta tsakanin Kamaru da Ukraine ba

Kyaftin din Kamaru, Samuel Eto'o, da ma wadansu fitattun 'yan wasan hudu, ba za su buga wasan sada zumuntar da kasarsu za ta buga da Ukraine ranar Lahadi ba.

Eto'o ba zai samu damar buga wasan ba ne saboda zai buga wa kungiyarsa ta Anzhi Makhatchkala wasan karshe na cin Kofin Rasha ranar Asabar.

Su ma Alexandre Song, da Allan Nyom, da Charles Itanje, da Benoit Assou-Ekotto, suna da wasannin da za su buga wa kungiyoyinsu.

Sai dai dukkanin 'yan wasan biyar za su shiga tawagar Indomitable Lions yayin wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya da za ta yi da Togo da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Itanje na da wasannin da zai buga wa kungiyarsa ta Paok Thessalonique ta Girka har zuwa ranar 2 ga watan Yuni, yayin da dan wasan tsakiya na Barcelona, Alexandre Song, da dan wasan aro na Granada, Allan Nyom, za su buga wasannin karshe na Gasar La Liga ta Spain ranar 1 ga watan Yuni.

Karin bayani