FIfa na babban taronta a Mauritius

Shugaban Fifa Sepp Blatter
Image caption Fifa za ta yanke hukuncin da zai iya hana wata kasa zuwa Gasar Kofin Duniya kan wariyar launin fata

An bude babban taron Hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa a kasar Mauritius ranar Alhamis din nan amma kuma sai ranar Juma za a fara gudanar da muhimman abubuwan da ke gaban Hukumar.

Abubuwan sun hada da zaben mukamin mace ta farko a kwamitin zartarwar Hukumar.

Masu takarar su ne shugabar Hukumar kwallon kafa ta Burundi Lydia Nsekera da Moya Dodd tsohuwar 'yar wasan Australia da kuma Sonia Bien-Aime ta Tsibran Turk and Caicos.

Ita kuwa Paula Kearn ta New Zealand ta janye daga takarar ta neman wa'adin shekaru hudu.

Haka kuma za a duba batun karin hukuncin laifin wariyar launin fata a wasanni.

Hukuncin zai kunshi hana dan wasa akalla wasanni 5, su kuma kungiyoyi da kasashe ka iya fuskantar wasa ba tare da 'yan kallo a fili ba.

Da rage maki da kuma hana shiga gasa ciki har da Gasar Kofin Duniya.

Karin bayani