Ingila da Brazil sun yi canjaras

Brazil da Ingila
Image caption Ingila ta kwaci kanta a hannun Brazil a Maracana

A ranar Lahadin nan anyi wasannin sada zumunta na kwallon kafa a tsakanin kasashe dabam dabam.

Ga yadda wasannin suka kasance.

Lesotho 0 - 2 South Africa

R. of Ireland 4 - 0 Georgia

Ukraine 0 - 0 Cameroon

USA 4 - 3 Germany

Brazil 2 - 2 England

Algeria 2-0 Burkina Faso

Sudan 0-0 Tanzania

A wasan da aka yi tsakanin Brazil da Ingila a filin wasa na Maracana na Brazil wanda aka sake budewa bayan gyaran da aka yi masa.

Brazil ce ta fara cin Ingila ta hannun Fred a minti na 57, kafinChamberlain ya rama a minti na 67.

Sai kuma Rooney ya ci wa Ingila kwallo ta biyu a minti na 79, sannan kuma Paulino ya farke a minti na 82.

Karin bayani