Premier ta baiwa Chelsea hakuri

Jose Mourinho
Image caption Chelsea da magoya bayanta na fatan komowar Jose Mourinho

Hukumar Gasar Premier ta bai wa Chelsea hakuri bayan da ta buga wani labari a shafinta na Intanet cewa Jose Mourinho ya koma Chelsea.

A ranar Lahadin nan aka sanya labarin da kwanan watan Litinin amma kuma aka cire shi daga baya.

Kakakin hukumar ta Premier ya ce an sanya labarin ne bisa kuskure kuma ana ankarar da su suka janye shi.

Ya kara da cewa hukumar ta Premier ba ta da wata masaniya takomawar Mourinho Chelsea ko kuma wata sanarwa game da hakan.

A ranar Asabar Mourinho da Real Madrid suka kawo karshen kwantiragin kociyan na shekaru 3 bayan wasansa na karshe da Osasuna da ya jagoranci kungiyar ta yi galaba da ci 4-2.

Ana ta rade radin kociyan zai koma kungiyar wadda ya kama aiki da ita a 2004 ya kuma jagorance ta ta dauki kofin Premier sau biyu a 2005 da 2006.

Daga nan ne kuma ya bar ta inda ya koma Inter Milan a 2008.

Karin bayani