Alonso ya fice daga tawagar Spaniya

Xabi Alonso
Image caption Xabi Alonso yana daga cikin 'yan wasa uku da suka fita daga tawagar Spaniya

Dan wasan Real Madrid Xabi Alonso ya fice daga tawagar 'yan wasan Spaniya da za ta je gasar Zakarun nahiyoyi.

Tsohon dan wasan tsakiyar na Liverpool ba zai je gasar ba saboda ciwon da ya ji a matsematsinsa.

Alonso yana daga cikin 'yan wasa uku da aka fitar daga tawagar da ta kunshi 'yan wasa 26.

Sauran 'yan wasan biyu su ne Javi Garcia na Manchester City da Benat Etxebarria na Real Betis.

Fernando Torres na Chelsea da dan wasan Arsenal Santi Cazorla na daga 'yan wasa 7 da ke wasa a Ingila da aka zaba a tawagar ta Spaniya.

Sauran sun hada da Pepe Reina na Liverpool da Cesar Azpilicueta da Juan Mata na Chelsea.

Sannan kuma da Nacho Monreal na Arsenal da David Silva na Man City.

Da farko dai kociyan Spaniyan Vicente del Bosque ba ya gayyatar Torres mai shekaru 29 a tawagar 'yan wasan kasar a baya bayan nan.

Amma kuma bayan da dan wasan ya ci wa Chelsea kwallaye 23 a bana kociyan ya ce ya kamata ya gayyace shi da shi da Martinez na Bayern Munich.

Za a yi gasar ta zakarun nahiyoyi ne daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa ranar 30 ga watan na Yuni a Brazil.

Zakarun nahiyoyi 6 ne ke zuwa gasar da ake yi bayan shekaru 4, hadi da kasar da ta ke rike da Kofin Duniya da kuma wadda za ta karbi gasar ta gaba.

Karin bayani