Jose Mourinho ya zama kocin Chelsea

Image caption Wannan shi ne karo na biyu da Mourinho ke zama kocin Chelsea

An nada Jose Mourinho a matsayin sabon kocin Chelsea a karo na biyu.

Mourinho, mai shekaru 50 a duniya, ya maye gurbin Rafael Benitez bayan ya bar Real Madrid.

Ya sanya hannu a kwantiragin shekaru hudu da kulob din.

Chelsea ta lashe Gasar Premier sau biyu karkashin jagorancin Mourinho lokacin wa'adinsa na farko wanda ya kare a watan Satumbar shekarar 2007.

Babban jami'in Chelsea,Ron Gourlay, ya ce Mourinho mutum ne da ke da matukar farin jini a kulob din, yana mai cewa suna fatan sake aiki da shi.

Karin bayani