Neymar ya kammala komawa Barcelona

Neymar Barcelona
Image caption Nyemar ne ake ganin zai zama dan wasan Brazil da zai fi fice a Gasar Kofin Duniya ta 2014

A ranar Litinin din nan matashin dan wasan Brazil Neymar ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru biyar da Barcelona akan fam miliyan 48 da dubu 600.

Dan wasan mai shekaru 21 ya sanya hannu a yarjejeniyar ne bayan ya tsallake gwajin lafiyarsa da likitocin Barcelonan suka yi masa.

An gabatar da dan wasan a gaban dubban magoya bayan klub din a filin wasansu na Nou Camp.

Neymar ya ce ya gode wa ubangiji da ya cika masa burinsa na yin wasa tare da zakaran 'yan kwallon duniya Messi.

Ya ce ba karamar martaba ba ce ya yi wasa a kungiya daya da manyan 'yan wasa irin su Messi da Xavi da Iniesta.

Karin bayani