Eto'o ba zai buga wasan Togo ba

Samuel Eto'o
Image caption Likitan Anzhi ya bukaci da a bar Samuel Eto'o ya huta

Kyaftin din Kamaru Samuel Eto'o ba zai buga wasan da Kasarsa za ta yi da Togo ba a Lome na neman zuwa gasar Kofin Duniya ranar Lahadi saboda raunin da ya ji.

Sai dai ana ganin dan wasan zai iya shiga wasan da Kamarun za ta yi na gaba da Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo a mako na sama.

Eto'o ya ji rauni ne a cinyarsa a lokacin wasan karshe na Kofin Kalubale na Rasha wanda kungiyarsa Anzhi Makhachkala ta yi da CSKA Moscow ranar Asabar.

Mai horad da 'yan wasan Kamarun Volker Finke ya ce klub din na Eto'o ya bukaci da a bar dan wasan ya huta na wasu makwanni, saboda haka ba zai yi wasan na Togo ba.

Ya kara da cewa, ''amma ina da tabbacin zai yi wasa na gaba bayan wannan da Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo ranar 16 ga watan Yuni a Kinshasha.''

Kamarun ita ce ta daya a rukuni na tara wato Group I da maki 6 Libya na bi mata baya da maki 5, yayin da Congo ta ke da maki 4 ita kuwa Togo na da maki daya kawai.

Karin bayani