Najeriya ta yi nasara akan Kenya

'Yan wasan Najeriya
Image caption Najeriya ta yi galaba akan Kenya duk da rashin wasu 'yan wasanta

Najeriya ta yi nasara a wasanta da Kenya na neman zuwa gasar Kofin Duniya da ci 1- 0 a Nairobi.

A cikin minti na tamanin da daya ne Ahmed Musa ya ciwa Najeriyar kwallon.

Nasarar ta bai wa Najeriya damar ci gaba da zama ta daya a rukunin na shida wato Group F da maki 8.

A karawarsu ta farko a watan Maris da aka yi a Calabar ta Najeriya sun tashi kunnen doki 1-1.

A daya wasan rukunin da aka yi tsakanin Malawi da Namibia an tashi 0-0 ba ci.

Malawin wadda kafin wasan take da maki 5 dai-dai da Najeriya da kuma aka yi wasan a gidanta ita ma ta ci gaba da rike matsayi na biyu a rukunin, da maki 6 yanzu.

Karin bayani