Martinez ya zama kocin Everton

Roberto Martinez
Image caption Wigan ta ce ba za ta taba mantawa da gudunmawar Roberto Martinez ba

Everton ta nada mai horad da 'yan wasan Wigan Roberto Martinez a matsayin kociyanta kan kwantiragin shekaru hudu.

Kociyan ya maye gurbin David Moyes, wanda ya tafi Manchester United wadda ita kuma kociyanta Sir Alex Ferguson ya yi murabus daga aikin horad da 'yan wasa.

Martinez mai shekara 39 dan Spaniya ya dauki Kofin FA da Wigan amma kuma ya bukaci barin klub din bayan ya kasa kare shi daga faduwa daga Premier.

Sabon kociyan ya yi wa Everton alkawarin kai su ga matakin zuwa gasar Zakarun Turai, bayan an yi masa alkawarin bashi kudaden sayen sabbin 'yan wasa.

Sannan kuma ya nada dan wasan Ingila na baya Phil Jagielka a matsayin sabon kyaftin din kungiyar domin ya maye Phil Neville wanda kwantiraginsa na shekaru 8 zai kare a karshen watan nan.

A watan da ya gabata ne Martinez wanda Wigan ta dauke shi aiki bayan ya kai Swansea gasar lig din kasa da Premier ta Championship daga League One ya bukaci tafiya bayan shekaru 4 daga Wigan din.

Martinez wanda ya buga wa Wigan wasa sau 180 tsakanin 1995 da 2001 ya dawo a matsayin kociya bayan shekaru 8.

Kafin ya karbi aikin horad da Wigan din ya rike Swansea daga 2007 zuwa 2009.

Karin bayani