Brazil ta sake yin kasa a jerin Fifa

Tutar FIFA
Image caption Fifa ta fi bayar da maki ta amfani da wasannin gasa akan na sada zumunta

Fifa ta fitar da jerin sunayen kasashen da ke kan gaba a kwallon kafa na watan Yuni, inda Brazil ta sake yin kasa zuwa matsayi na 22 da bata taba zuwa ba.

Brazil ta yo kasa da mataki uku akan inda take a baya, yayin da take shirin karbar bakuncin gasar Kofin Duniya a shekara mai zuwa.

Galibi kasar tana wasannin sada zumunta ne kawai da suka hada da wanda ta yi 2-2 da Ingila, kuma wasan sada zumunta ba ya sa kasa ta samu maki mai yawa a rahotan na Fifa.

Zakarun Duniya da kuma Turai, Spain sun ci gaba da zama daram a matsayi na daya tun watan Agusta na 2011, sai Jamus da Argentina da kuma Crotia da ke bin baya.

Netherlands ta samu ci gaba da mataki hudu ta zama ta biyar, sai Portugal sannan kuma Colombia ta 7, yayin da Italiya ta ke ta 8.

Ingila ta yo kasa da mataki biyu ta zama ta tara, Ecuador ta cike matsayi na goma.

Belgium da Bosnia-Herzegovina da suke jagorancin rukunoninsu na neman zuwa gasar Kofin Duniya sun kai matsayin da ba su taba kaiwa ba na 12 da kuma 15.

Ivory Coast wadda daman ita ce ta daya a Afrika ta yo kasa da matsayi daya yanzu ta zama ta 13, yayin da Ghana ta samu ci gaba a matsayin ta biyu a Afrika kuma ta 21 a duniya.

Mali ita ma ta dago sama da mataki daya inda take ta uku a Afrika ta 23 a duniya kasa da Brazil.

Tahiti wadda ita da Najeriya za su wakilici Afrika a gasar Zakarun Nahiyoyi da za a fara ranar 15 ga watan nan a Brazil ita ce ta 138 a duniya, yayin da Najeriyar ta ke ta 31 a duniya kuma ta 4 a Afrika.

Ga jerin yadda kasashen su ke:

1 Spain 2 Germany 3 Argentina 4 Croatia 5 Netherlands

6 Portugal 7 Colombia 8 Italy 9 England 10 Ecuador

11 Russia 12 Belgium 13 Côte d'Ivoire 14 Switzerland

15 Bosnia-Herzegovina 16 Greece 17 Mexico 18 France

19 Uruguay 20 Denmark 21 Ghana 22 Brazil 23 Mali 24 Czech Republic

25 Chile 26 Montenegro 27 Sweden 28 USA 29 Norway 30 Peru