Ingila bata tabuka komai ba - Pearce

Mai horar da 'yan wasan Ingila na 'yan kasa da shekaru21, Stuart Pearce
Image caption Staurt Pearce

Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 21 na Ingila, Stuart Pearce yace kungiyar bata tabuka komai ba a karawarsu da Italiya.

An soke kwallon ingila guda daya saboda alkalin wasa yace kwallon ta taba hannun Lorenzo, wanda ya buga ta a bugun tazara.

Hakan ya baiwa Italiya nasara a bude gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta 'yan kasa da shekaru 21, wanda aka yi a Tel Aviv.

Pearce ya bayyana cewa " Kwata-kwata bamu yi wani abin a zo a gani ba a karawar, 'yan wasan sun san haka, shi yasa ma wadanda suka fi mu suka lashe wasan."

Ya kara da cewa "Abin da kawai ke dan faranta rai, shi ne duk da cewa ba mu yi wasa mai kyau ba, an tashi ne da ci daya da nema."

Kocin yace akwai bukatar kungiyar ta yi amfani da kwana biyun da take da shi, kafin wasa na gaba domin tabbatar da cewa 'yan wasan sun yi wasa mai kyau.

A ranar Asabar mai zuwa ne kungiyar za ta kara da takwararta ta Norway, gabannin kammala wasa a rukunin A da mai masaukin baki Israila a ranar Talata mai zuwa.