Serena da Sharapova za su fafata

Maria Sharapova
Image caption Sharapova da Serena na neman sake daukar Kofin gasar Faransa

Serena Williams gwana ta daya a duniya ta kama hanyar sake daukar kofin gasar tennis ta Faransa Roland Garos a karo na biyu inda za ta hadu da mai rike da kofin a Maria Sharapova.

Ba Amurkiya Serena za ta hadu da Sharapova 'yar Rasha gwana ta biyu bayan da ita Serenan ta lallasa Sara Errani ta Italiya a wasan kusa da na karshe da maki 6-0 , 6-1.

Rabon Serena da zuwa wasan karshe na gasar tun a shekara ta 2002 da ta dauki kofin.

Ita kuwa Maria Sharapova ta samu damar sake zuwa wasan na karshe ne bayan da ta sha da kyar a hannun Victoria Azarenka 'yar Belarus da maki 6-1, 2-6, 6-4

A ranar Asabar ne za a yi gumurzun gwanayen ta daya da ta biyun, Maria na neman juyawa da kofin ita kuwa Serena na neman sake rikar kofin.