Arsenal za ta kashe makudan kudade

Arsenal
Image caption Arsenal

Shugaban kulob din Arsenal Ivan Gazidis ya ce kulob dinsa a shirye yake ya kara yawan kudaden da yake kashewa a kakar wasa mai zuwa.

Ko da aka tambaye shi ko Arsenal din za ta iya kashe Fam miliyan 20 akan siyan dan wasa guda, tare da biyansa albashin Fam 200,000 duk sati, sai ya ce: "kwarai ma kuwa zamu iya yin hakan, kai fiye ma da haka."

Sai dai ya yi gargadin cewa kocin kulob din Arsene Wenger, wanda Gazidiz ya ce "zai jima sosai a kulob din", ba lallai ba ne ya kashe wadannan kudade.

"Za a kashe kudaden ne a kan irin 'yan wasan da Arsene ya yarda da su" In ji Gazidis.

" Shi mutum ne da bai damu da farashin dan wasa ba, yana duba abinda ya dace ne kafin ya yanke hukunci akan sa, ba wai shaharar dan wasa ba ko kudin sayensa."

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba