An hana kallon wasannin waje a Argentina

Image caption An hana masoya kwallon kafa kallon wasannin waje a Argentina

A karon farko a tarihin kasar Argentina, an dakatar da masoya kwallon kafa daga halartar wasannin waje a cikin kasar.

Wannan matakin ya biyo bayan mutuwar wani dan kallo bayan da aka yi arangama tsakanin yan kallon da kuma 'yan sandan kwantar da tarzoma.

Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce yan kallon cikin gida ne kawai za a bari su shiga filin wasanni har zuwa lokacin da za a dauki sababbin matakan kawo karshe tashe-tashen hankula.

Wannan zai shafi wasannin zagaye na biyu na kasar wanda a karshen mako yake hada dubban masoya kwallon kafa a filayen wasanni a fadin kasar.

Karin bayani