Fabregas ya soki danganta shi da Ingila

Image caption Fabregas ya soki rahotan dangantashi da komawa Ingila

Dan tsakiyar nan na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Cesc Fabregas, ya soki lamirin rahotannin da ke danganta shi da komawa Ingila.

Dan wasan mai shekaru 26, ya rattaba hannu da kulob din Gunners yana dan shekara 16.

Ya bayyana a wasanni har sau 303 ga kulob din a shekaru takwas inda ya zura kwallaye 57; ya kuma zama dan wasa mai mafi karancin shekaru.

A Kakar wasannin bara Fabregas ya buga wasanni 30 cikin wasanni 38 amma an yi haftar sa sau 16.

Karin bayani