Chelsea za ta bada £18m don sayen Andre Schurrle

Andre Schurrle
Image caption Dan wasan kwallon kafa Andre Schurrle

Andre Schurrle na gab da zama dan wasan farko da Jose Mourinho zai dauka tun bayan komawarsa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Chelsea ta cimma matsaya da kungiyar kwallon kafa ta Bayer Leverkusen kan dan wasan gaba na kasar Jamus watau Andre Schurrle akan fam miliyan 18.

Schurrle mai shekaru 22, yanzu zai tattauna da Chelsea tare kuma da duba lafiyarsa kafin ya soma taka leda a kulob din.

A ranar 3 ga watan Yuni aka tabbatar da Mourinho a matsayin sabon kocin Chelsea sai dai kungiyar kwallon kafa ta Bayer Leverkusen ta ce tun kafin a nada Mourinho ne kungiyar Chelsea ke zawarcin Schurrle.

Dan wasan ya ci wa kulob din Bayer Leverkusen kwallaye 11 a wasanni 34 a kakar wasanni ta 2012-13 kuma kulob din shi ne ya zama na uku a gasar Bundesliga.