Owen Coyle zai maye gurbin Martinez a Wigan

Wigan
Image caption Tsohon kocin Wigan Roberto Martinez

Za a nada tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Bolton Wanderers Owen Coyle a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Wigan kan kwantaragi mai tsawon wa'adi na watanni 12.

Dan wasan dan yankin Scoltand mai shekaru 46 zai maye gurbin Roberto Martinez a filin wasa na DW, bayan dan kasar Spain din ya sauya sheka zuwa Everton.

Coyle ya rike mukamin kocin Bolton daga shekarar 2010 zuwa 2012 kafin a koreshi watanni biyar da suka gabata bayan martabar kulob din ya fadi a gasar firimiya.

Shugaban Wigan Dave Whelan mai shekaru 76, ya shaidawa BBC cewa sun cimma matsaya da Coyle.

A kakar wasanni da ta gabata ne kulob din na Wigan ya fuskanci koma baya, sai dai nasarorin da ya samu a gasar wasannin FA a watan Mayun da ya gabata ya sa za su yi wasa a gasar Europa.