Kinnear ya zama daraktan Newcastle

Image caption Joe Kinnear ya ce zai sayo sababbin 'yan wasa

Tsohon kocin Newcastle United, Joe Kinnear, ya bayyana cewa an nada shi a matsayin sabon daraktan wasannin kwallon kafa na kulob din.

Mista Kinnear, mai shekaru 66 a duniya, ya yi shugabancin kulob din a kakar wasa ta shekarar 2008 zuwa 2009 .

Ya bayyana cewa zai taka rawa wajen sayowa kulob din sababbin 'yan wasa.

A cewarsa, "Mun kammala batun dawowa ta kulob din. Na sanya hannu a kan kwangilar dawowa ta da mai kulob din, Mike Ashley, ranar Lahadi. Ina sa ran ganawa da kocin kulob din, Alan Pardew, a makon da muke ciki."

Karin bayani